[facebook] Yadda ake canza password na facebook cikin sauki - 2020

Assalamualaikum, barkanmu da sake haduwa daku acikin wannan shafin mai albarka,

Kamar dai yanda kuka sani wannan shafin shafine da yake kawo maku rubuce-rubuce akan fasahar zamani.

dalilin dayasa zan danyi maku tsokaci game da yanda ake canza password sabida a halin yanzu ya zama dole ka riqa yawan canza password dinka na facebook account dinka, saboda yanzu idan bakai wasa za'a kwamushe maka account, kanaji kana gani zaka hakura, dalilin da yasa dole kaji wani iri na rasa facebook account dinka, saboda zakayi tunanin cewa kowa yasanka da wannan account din, sannan kuma ka rasa wasu daga cikin abokanka wanda kun riga kun san juna

Nasan wasu zasu tambayeni akan cewa menene sukeyi da account din mutum bayan sun kwacewa mutum?

Amsar wannan tambayar tanada matukar muhimmanci kasan dalili, saidai kuma bamu da isashshen lokacin da zamu yi maku akan hakan, saboda ba akan shine muke rubutun ba, sai kuma bari muyi maku bayanin kadan daga cikin dalilan da yasa hacker suke kwamushe wa mutun account dinsa


Karanta wannan: Yadda zaka kir-kiri facebook account
Yadda ake samun kudi ta facebook
Yadda ake whatsapp biyu a waya daya

Wasu suna yin hakane domin su bata maka suna a gari, abinda nake nufi zata iya yiwuwa kai mutumin kir-kine ka nayin wa'azi da sauransu a cikin shafinka na facebook, to sai su rabaka da wannan account din naka sai sukama yin abubuwan da basu dace ba a cikin facebook din naka

Wasu kuma sunayin hakane domin su samu kudi da kai, zasu iya rabaka da account dinka suce sai ka biyasu kaza sannan zasu baka account dinka,

Wani lokaci kuma 'yan sanda ne : kamar dai yanda kuka sani 'yan sanda sukan kwace wa mutum account dinka na facebook idan basu yarda da wannan mai account din ba,

Wadannan sune kadan daga cikin dalilan da yake sawa ake yin wa mutum hack din account dinshi, akwai hanyoyi da dama wanda suke ba, amma zanyi maku bayani a posting na gaba insha Allahu, sannan kuma zanyi maku bayani akan yanda zaka magance wadannan matsalolin,

daga cikin hanyoyin da zaka magance wadannan matsalolin shine yanzu na zo maku da kwara daya, saboda kada kayi tunanin cewa saboda ba'a san password dinka ba baza'a iya yin hack din account dinka ba, sam-sam wannan batu ba haka yake ba, saboda mai son kayanka yafika dabara


Karanta wannan: Menene google analytics?
Yadda ake kasuwanci ta whatsapp
Ma'anar kalmar protocol a computer
Abubuwa 3 da zakayi kafin ka nemi apply na adsense
Yadda zaka kirkiri facebook account cikin sauki



Tayaya zan canza password na facebook account dina?

Dama wannan shine taken darasin mu, to dafarko dai hanyoyin da ake canza password na face book guda biyune

Wato akwai facebook wanda akeyin shi da application, (abinda nake nufi, shi facebook na application dole sai kayi downloading dinshi), sannan kuma akwai facebook wanda akeyinshi akan waya, to duka zamuyi maku bayanin yanda ake canza password a cikinsu

Yanzu zamu fara da facebook na application

Da farko dai ka shiga cikin facebook dinka kamar haka
Bayan ka shiga sai ka ta6a gurij da kaga nayi mashi alama, zakaga ya kawoka wani shafi kamar haka
Kamar dai yanda kukaga wannan hoton na sama, bayan ya nuna maku haka, sai ka danna gurin da aka rubuta "Setting", bayan ka shiga zakaga ya qara kawoka wani shafi kamar haka

Kamar dai yanda kukaga wannan hoton na sama haka zakaga ya nuna maka acikin wayarka, sa ka sake danna gurin da aka rubuta "Security and Login", bayan ka shiga zakaga ya qara kawoka wani shafi kamar haka


Kamar dai yanda kukaga wannan hoton na sama, wato akwai, Current password, New password, Retype New password.


Current password: shi current password ananne zaka sanya tsohon password dinka wanda kake aiki dashi

New password: shikuma New password ananne zaka sanya sabon password din da kakeson sawa.

Re-type New password: shikuma Re-type New Password ananne zaka mai-maita sabon password din daka sanya,

Duk bayan ka gama sai ka danna "Save changes" bayan ka danna zakaga ya kawoka wani shafi kamar haka

Kamar dai yanda kuka gani a wannsn hoton na sama, da zaran ka danna shikenan ka gama canza password dinka na facebook, yanzu da zaran ka tashi shiga facebook dinka, to da sabon password dinka zakayi amfani

Sai kuma yanda ake canza password na facebook akan waya ko opera
Wato kamar dai yanda nace maku facebook akwai na application, sannan kuma akwai na kan waya, already mun riga munyi bayanin na application, yanzu kuma zamuyi maku bayanine akan na kan waya ko opera

Saboda da na kan waya da na Opera duk daya suke,
Da farko dai zakaje kan wayar ka ne, inda kakeyin browsing sai ka rubuta Www.m.facebook.com ko kuma www.m.fb.com ko kuma Ka danna nan kai tsaye zai kaika shafin facebook din, amma kuma idan ta opera ne ka shiga to base karubuta ba, zakaga facebook, kawai dannawa zakayi sannan kayi login na account dinka, bayan kayi login zakaga ya kawoka shafinka na facebook kamar haka
Kamar dai yanda kuka gani a hoton da yake sama, to bayan kashiga cikin facebook dinka, sai kayi can qasa, a cikin facebook dinka, zakaga ya kawoka wani shafi kamar haka
Kamar yanda kuka gani a wannan hoton na sama, sai ka dannan gurin da aka rubuta "Setting & Privacy" kamar dai yanda kukaga nayi mashi alama da blue

Bayan kun shiga setting & privacy zakuga ya nuna maku wani guri kamar haka
Kamar dai yanda kuka gani a wannan hoton na sama, sai ka latsa gurin da aka rubuta "Security and login"
Bayan kashiga zakaga ya nuno maka gurin da zaka canza password dinka kamar haka
Kamar yanda kuka gani, to ba sai na qara yi maku bayani akanshi ba, saboda already munriga munyi bayani a sama, bayan ka kammala sai ka danna "Save Changes" shikenan ka gama
Ammafa idan ka lura duk kusan iri daya ne da na kan wayar da kuma na application din, ban-bancinsu kadan ne, dalilin da yasa nayi bayani akan dukansu, saboda zata iya yiwuwa wani bai san yanda zaiyi wani daga cikinsu ba
Da fatan an fahimta, zan dakata anan, sai kuma a rubutu na gaba insha Allahu zamu dora daga inda muka tsaya,
Kuyi shiyarin domin wasuma su qaru





Facebook: KUYI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK

Whatsapp: ZAKU IYA BIYOMU TA WHATSAPP

Twitter: KUYI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER

Instagram: KUYI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM

Call & Message: +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post