Yadda ake kirkiran android apication na Gallary da wayar android














Wannan shafi mai dumbin albarka Wanda ke fadakar da jama'ah abubuwan da suka shafi internet da social media.

Zamu yi cikakken bayani ne kan yadda zaka kirkiri android application na hotuna da wayar ka ta android da waya, a Wannan darasin kuma cikin kankanin lokaci.

Akwai hanyoyi da dama wadanda ake yin android application dasu, ga wasu daga ciki:

1. Akwai wadanda a ke yi da yaren programming/coding.

2. Akwai wadanda ake Gina su a kan website da ake kirkiran applications

3. Akwai wadanda kuma a cikin wani application ake kirkiran su.

Akan na 3 zamu mai da hankali a yanzu.

Abubuwan da ya kamata ka sani a kan android application

1. Akwai wadanda dole Sai da computer za a yi su, kwata-kwata baza su yiwu a kan waya ba. Computer ma ba ko wace iri zata yi wanin ba.

2. Akwai wadanda sai ka kashe kudi kafin kayi, wasu kuma kyauta ne.

3. akwai website wadanda ake application a kan su kyauta tun daga farko har karshe

4. Wasu website din kuma zasu baka daman kirkiran application free guda daya kafin ka kara yin wani sai ka biya su.

Abubuwan da zaka tanada don kirkiran free pictures android application

Abu na farko wayar ka ta zama da data Wannan shine babban abunda a ke bukata domin sai kayi downloading na application da zamu yi amfani dashi.

Yadda zaka sauke application da zamu  yi amfani dashi

Kamar yadda na fada muku tun farko da wani application zamu yi amfani kuma baida nauyi.

Sunan Wannan application shine APK Creator, zaka iya zuwa play store ka sauke ko kuma kabi Wannan link kai tsaye zai kai ka sai ka sauke Download Apk creator Now

Yadda zaka kirkiri application na hotuna

1. Bayan ka sauke sai ka bude zai kawo ka Wannan shafi dake kasa


Da Wannan application Ana kirkiran application ne guda uku Kuma duk zan yi muku bayanin yadda a keyi daya bayan daya A darussa mabambanta, kenan rubutu na na gaba zai iya kasancewa akan Gift app.

2. Idan ya kawo ka Wannan shafi sai ka shiga Abu na farko wato create a picture apk zai kawo ka nan.


Sai ka cike wadannan gurare, ka rubuta sunan application, cover image da sauran su.

A group 1 sai ka rubuta sunan hotunan misali kamar ace sunan folder.

3. Gurin alamar Tarawa + zaka taba, nan take zai kai ka kan hotunan dake kan wayar ka sai ka saka wadanda kake so daya bayan daya.

4. Bayan ka saka su idan kana bukatan saka wasu hotunan na daban sai ka danna Add Group ka sawa wadannan hotunan sunan da ya dace dasu, sai kabi Wannan step ka Dora su a kan app din ka.

5. Bayan ka Dora hotunan ka sai ka danna create APK.

Idan ya gama creating zai nuna maka success sai ka taba close.

6. Ka shiga view a sama ta gefen dama za kaga application da ka kirkira sai ka installing din shi.

Anan zan dakata sai a darasi na biyu zamu sake hadewa.




Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK



Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHASAPP



Twitter: YI FOLLOWING DINMU TA TWITTER



Instagram: YI FOLLOWING DINMU TA INSTAGRAM



Call & Message: +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post