Yadda za kasa password wa applications dake kan wayar ka













A wannan darasi zamu yi bayani ne game da yadda zaku sa password a Applications dake kan wayoyin ku cikin yan mintuna kalilan.

Karanta wannan: Kowa zai iya zama blogger?


Wannan tambayar tana zuwa ne akan dalilin da bai wuce yin maganin masu karban danin wayar ba, wani zai iya Neman Aron wayar ka gashi kuma baza ka iya hana shi ba kuma kila akwai wasu sirruka Wanda baka so kowa ya gani.

 Wani da zaran ya karbi wayar ka abunda yake fara dubawa shine chatting na watsapp din ka, hawa Facebook, shiga kan  gallary don kallon hotunan dake kan wayar.

Wani kuma idan ya dauki wayar ka abunda zai fara dubawa shine lambobin waya dake kan wayar, Received da Dial call duk sai ya duba kawai saboda tsabar sa ido, eh mana toh idan ba sa ido ba me ya kai ka yin abunda baka da alaka dashi?

Daga cikin dalilai da yake sa wasu yin irin wannan binciken shine kawai su damuwar su suga wani aibin ka, Wanda irin Wannan binciken ko addini ma bai yadda dashi ba, kawai kace sai ka nemi aibin wane baida amfani ko kadan sai a kiyaye.

Karanta wannan: Koyi html, css, java acript da programming cikin sauki a offline w3school


Wannan dalilin ne da kuma tambayoyi da korafe-korafe da wasu 'yan uwa suke yi na Neman yadda zasu magance Wannan matsalar ya jawo hankali na nayin Wannan takaitaccen bayanin don magance matsalar.

Yanzu zan yi bayani filla-filla kan yadda za kasa password ko kuma security wa duk applications da suke kan wayar ka.

Da wani application zamu yi amfani don haka sai ka kunna datan wayar ka ka dauko Wannan application a play store, bayan kayi installing din shi duk wani amfani dashi da zaka yi offline ne ma'ana ba sai ka kunna data ba.

Sunan application da zamu yi aiki dashi shine Applock, Ana abubuwa da yawa dashi sai dai a yanzu baza mu bar Wannan maudu'i da muka dauko ba sai daga baya zan yi bayani akan sauran aikin shi.


Karanta wannan: Website Guda 11 wadanda zaka samu hotuna kyauta don dorawa a blog site


Yadda zaka sauke Applock akan wayar ka

Wannan Abu mai sauki ne na San ka saba sauke applications a kan wayar ka.

Da farko zaka shiga Wannan link Download Applock Now. Idan ka shiga zai kai ka kan Application din a play store Sai ka sauke shi.

Ko kuma kaje play store ka dauko Applock idan bin Wannan link zai baka wahala kenan

Yadda za kayi amfani da Applock

Bayan ka sauke shi sai ka shiga kan application din, a nan za kaga sunayen duk applications da kake amfani dasu a kan wayar ka.

Ka duba gefen dama na ko wane application za kaga alamar kwado (lock) sai ka danna Wanda kake son sawa password.

Domin neman karin bayani sai ka aje mana comment a kasan wannan posting din








Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK



Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP



Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER



Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM



Call & Message :  +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post