
Kafin ka samu AdSense a shafin ka dole ne sai ka cika dokokin da AdSense din suka bayar wa masu bukatan su.
Anan zan yi bayanin guda uku daga cikin su kuma masu muhimmanci a takaice:
Karanta wannan: ABUBUWAN DA YAKAMATA KAYI BAYAN KA MALLAKI WEBSITE
1. Kana da Rubuce-rubuce Wanda ka kirkira da kan ka?
Ba zai yiwu ka cika shafin ka da rubuce-rubucen wasu kuma kayi mafarkin samu approved na Google AdSense ba.
Dole ne sai kayi aiki tukuru na kirkiran original content ka rika dorawa a website ko blog site din ka, ka cire tunanin kofan rubutun wasu zaka Dade baka samu abunda kake nema ba.
2. Rubuce-rubucen ka basu kaucewa dokokin Google AdSense ba?
Ba wai rubutu original kadai ake bukata ba dole sai kabi dokokin su na yin rubutu.
Don Neman Karin bayani zaka iya zuwa Help center nasu ko kayi search na privacy policy na Google akan AdSense a nan zaka samu cikakken bayani akai.
Karanta wannan: Idan na chanja template adsense dina zai samu matsala?
Yadda zaka kirkiri facebook account cikin sauki
Hanyoyi guda 8 da zaka bi domin koyon engineering
How computer is working?
yadda ake whatsapp guda biyu a waya daya
Menene google analytics?
Yadda zaka kirkiri Gift android application da wayar ka
Kowa zai iya zama blogger?
3. Shekarun ka na haihuwa sun kai sha takwas (18)?
Google AdSense basa approving na Wanda bai kai shekara 18 ba kamar yadda yake a tsarin su.
Wani zai iya tambaya kamar haka 'to ta ya zasu gane shekaru na?'
Ai Wannan mai sauki lokacin da kake bude email ai akwai gurin da zaka saka shekarun haihuwar ka har da kwanan wata.
Yanzu kuma da kake kirkiran blog har zuwa apply na AdSense duk da email kake yi ko? Uhmm! Na San dai Na share maka tantama to ai shikenan.
Abun lura: Idan kai Dan kasa da shekara 18 ne, zaka iya kasancewa da iyaye ko wadanda suke lura da Kai zaka iya apply da Google account din su. Idan AdSense suka karbi account din na su toh Duk wani payment zai kasance da account din sune, kenan da Adult ake harkallan.
Da fatan za'a kiyaye.
Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK
Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP
Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHFINMU NA INSTAGRAM
Call & Message: +2349036117711
Tags:
ADSENSE