Assalam barka da zuwa Wannan shafi mai albarka da fatan kuna jin dadin kasancewa damu.
Akwai tambayar dake yawo a kafofin sadarwa na zamani musamman dandalin Facebook, tambayar itace shin kowa zai iya zama blogger?
Kafin mu bada amsar Wannan tambaya ya kamata mu San wanene blogger tukuna.
Wanene blogger?
A takaicen takaitawa blogger shine Wanda ya mallaki shafin yanan gizo (blog site) kuma yake rubuce-rubuce a ciki ko na baiyana ra'ayin sa, tallata hajar sa da dai sauran su.
Akwai shafuka da dama wadanda ake kirkiran blog dasu musamman blogger da WordPress sune suka fi sanuwa sai dai akwai wasu dayawa, Blogger ne ya fara fitowa daga baya sai WordPress ya baiyana har zuwa yanzu da aka samu Kari.
Shin kowa ne zai iya zama blogger?
Amsar Wannan tambaya mai sauki ne, Duk Wanda yake iya karatu, Rubutu da bincike a yanan gizo zai iya zama blogger.
Kuma duk fannin daka dauka zaka yi blogging a kai ba bukatan wai sai ka San shi Dari bisa Dari Matukar kana da juriyan bincike ka fara rubuce-rubucen ka, Duk lokacin da kayi sabon bincike sai kayi posting a hankali site din ka zai habaka.
Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK
Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP
Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM
Call & Message: +2349036117711
Tags:
BLOGGING
