Yadda zakayi Please Call Me a Layin Glo cikin Sauki || Hausaweb.com.ng





Assalamualaikum, maraba da sake shiguwa wannan shafin mai albarka, wato "Www.Hausaweb.com.ng"
Kamar yanda kowa yasani cewa an kirkiri wannan shafin ne domin kawo maku abubuwa wadanda Suka shafi fasahar zamani da dai sauransu, Sannan kuma kowani rubutu mukanyishine a cikin Harshen Hausa, ta yanda 'yan uwana Hausawa bazasu sha wahalar karantawa ba.


Karanta Wannan : Idan na chanja Template Adsense dina zai samu matsala?


Ba tare da bata lokaci ba yau zanyi maku bayani ne akan yanda zakayi Please Call Me, 

Sai dai kuma yawancin mutane basu san dalilin da yasa kamfanin layuka Suka fitar da irin wadannan tsaruka na Please Call Me" ba , Dalili kuwa shine :- yawancin wasu mutane kudi yakan yanke masu adai-dai lokacin da Suke da bukatuwa na yin magana da wani, sai dai kuma rashin kudi yakansa kaga mutum ya hakura, sakamakon rashin kudi, koda kuwa magana ne akan yanda zai samu wasu kudade dole ya hakura, Lallai kuwa anan kaga kuwa kamfanin layuka ba karamin kyautawa sukayi mana ba, sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba,  Su kamfanin layin Glo ba kamar sauran layuka bane, Ba irin layin MTN bane da zakasamu damar tura rubutu har Kala daban daban, a'a shi Glo Abu daya ne kawai ake iya Turawa, kada na cikaku da surutu.


Idan kanason yin Please call me din a layin Glo sai ka Danna Wannan Code din dake kasa.


*125*Lambar wayar wanda kake son ya Kira ka #

Misali: mudauka wannan itace Lambar wayar da kake son kayi mashi Please call me, 07015501101, to sai ka Danna kamar haka.

*125*07015501101#

Lura: Sai dai kuma su layin Glo, sunada ka'idar yin please call me,
Ka'idar kuwa itace su Please call me din su sau biyar [5] ne kawai ake yi, amma idan kayi ya wuce haka to bazaiyi ba.


Wannan shine Darasin mu na yau, Da fatan kuna jin dadin kasancewa da wannan shafin namu na Hausaweb.com.ng , sannan kuma zaka iya Aiko mana da tambayar dabaka gane ba, ta hanyar yimana Comment a kasan Wannan posting din, ko kuma zaku iya biyomu ta kafafen sadarwa Gasu kamar haka :







Call&Message: +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post