A Cikin dan kankanin lokaci za ka iya kirkiran blogger site kaci gaba da rubuce-rubucen ka a ciki, blogging daya ne daga cikin hanyoyin kasuwanci kuma ana iya samun kudi, idan kana so ka Gina blog me kyau Wanda za ka ci riban shi to dole ne ka kashe kudi kamar na data da sayan domain, Koda yake ana samun domain na kyauta kamar .ga, .tk, .gq da sauran su.
Sai dai magana ta gaskiya kar ka biyewa na bati, ka cire kudi ka sayi domain don neman kudi sai da kudi, matukar baka kashe kudi wa blog ba toh kai ma ba wani kudin da zaka samu dashi.
Ana iya samun kudi da blog ta hanyoyi da dama, sai dai hanya mafi sauki shine amfani da AdSense, bayan ka gama tsara blog din ka za kayi register da google AdSense za su rika turo talle a blog din na ka ta wannan hanyar za ka rika samun kudin shiga.
Blogging yana da matukar tasirin isar da sako musamman a wannan zamani da fasaha ta kara bunkasa fiye da tunani, A da hanyoyin Isar da sako basu wadata ba akwai zamanin da ba a iya Isar da sako sai an taka kafa da kafa anje har garin da ake son Isar da sakon har aka fara samun ci gaba aka samu wayar salula ta yadda za kayi magana da kowa a fadin duniya daga inda kake.
Ana nan har aka samu internet da social media yadda ake rubuce-rubuce da tabka muhawara a wadannan kafafe na sada zumunta kamar Google, Facebook, tweeter, WhatsApp, Instagram da sauran su, Har zuwa baiyanan blogging da ake Isar da sakonni daban-daban kuma har ake samun 'yan chanji.
Akwai matakai daya kamata mutum yabi kafin Fara blogging wannan ne dalilin dayasa na tsamo guda hudu daga cikin su domin nayi bayani akan su, Ga abubuwa guda 4 daya kamata ka lura dasu kafin fara blogging:
- Ka nemi Domain mai dadin kira
Idan zaka fara blogging abu na farko da ya kamata ka fara tunawa shine Domain, dole ne ka nemi domain wanda za a yi saurin haddace shi, donain shine sunan site din ka, ka nemi suna mai dadi kuma mai sauki wanda duk mutumin da ya shiga site din sau daya zai haddace ko ya kama sunan.
Wasu sun dauki sunan domain a matsayin kamar abun ado, za kaga sun yi shi ba tare da kan gado ba, wannan kuskure ne ka nemi suna mai sauki ka sawa blog din ka.
- Ka tsara blog din ka
Dole sai ka tsara blog site kasa template me kyau Wanda zai kayatar da masu karatu, idan baka samu template mai kyau ba gaskiya mutane za su guji shafin ka.
- Kasan yadda za ka tsira daga masu Satan rubuce-rubucen ka
Me ya kamata kayi idan ana copying rubutun ka ba tare da izini ba? Kasan yadda za ka tsare su, kai ma ka guji sace fasahan wasu ka zauna ka kirkiri naka, Dole ne ka zama mai kirkiran rubutu ba wai me kofan na wasu ba saboda babu inda za kaje idan baka kirkira.
- Ka rika sharing zuwa social media
Ba dai-dai bane kayi rubutu me kyau a blog kuma ka tsaya kana jira a zo a karanta a'ah ka na yadawa (sharing) zuwa shafukan sada zumunta kamar su Facebook, WhatsApp, instagram da sauran su, Ta haka ne zaka Tara mabiya masu tarin yawa cikin kankanin lokaci kuma da Tara mabiya masu yawa ne zaka samu kudi.
- Blogging yana daukan lokaci kuma dole sai ka sa kwazo
Kafin ka fara blogging ka tambayi kan ka me yasa kake son farawa? Idan burin ka shine samun kudi online, maganar gaskiya blogging ba shine hanyar da zai kawo maka kudi kamar yadda kake zato ba, akwai hanyoyin da suka fi shi samun kudi, blogging yana daga cikin su sai dai shi yafi wuya.
Yana daukan lokaci me tsayi da aiki tukuri kafin ka samu mabiya dole sai kayi hakuri kuma kar kayi tsammanin samun kudi cikin kankanin lokaci.
Wannan shine takaitaccen bayani akan hanyoyin da ya kamata kabi don inganta blog din ka tun kafin ma ka kirkira.
Ci gaba da kasancewa da wannan shafi mai albarka don samun irin wadannan rubuce-rubuce masu fa'ida.
Ina fata rubutun ya amfanar, kuma zai sa ka shirya tsaf kafin fara blogging.
Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK
Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHASAPP
Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM
Call & Message: +2349036117711
Tags:
BLOGGING
