Idan na chanja template Adsense dina zai samu matsala?











Shin idan akwai adsense a blogger site,  idan aka chanja template me zai faru da adsense dake kan site din?

Wannan tambaya dake sama a na yawan samun ta a kafofin sadarwa na zamani musamman Facebook da watsapp sai dai ba kowa ne yake iya bada takamammen amsan ta ba.

Cikin Wannan darasi zamu amsa Wannan tambayar ba tare da wani bata lokaci ba.

Tabbas lokuta da dama ana wahala sosai kafin a samu approval na Google AdSense Wannan ne dalilin da yasa mutane suke yawan tambayoyi a kai saboda kar garin Neman kiba a samo rama.

Kafin mu amsa wannan tambaya ya kamata kasan ma'anar template da kuma adsense

Da farko, Menene template?

Template shine yake kayatar da blog kamar yadda kusan kowa ya sani,  a lokacin da aka kirkiri blog bayan an shiga kan blogger site din za a ga baida tsari ko kyan gani,  sai an dora template yake kasancewa da tsari hade da kyan gani.

Karin bayani akan template shine,  ana samun na kudi; wanda sa ka saya kafin ka samu daman dorawa a blog.
Akwai kuma na kyauta wanda shafuka da dama suna bada template a matsayin kyauta.

Template baya hawa kan blogger har sai an yi extract din shi, domin wani template din a zip file yake zuwa sai an yi unzip din shi.

Akwai wanda kuma yake zuwa a unzip din shi,  kenan ba sai an yi extract ba.
Kalmar unzip da extract duk yana nufin abu daya ne kar ka dauka ko akwai bambanci.

Nayi amfani da kalmomi biyun ne don kar kaji wani yayi amfani dashi a wani wajen ka rude ko ka tsaya tambayar bambancin su.

Menene amfanin Template?

Dora Template mai kyau  yana da matukar muhimmanci kuma yana kara kayatar da blog,  ga kadan daga cikin amfanin template a blogger site;

  • Yana karawa masu ziyartan shafin kwarin guiwan karanta rubuce-rubucen cikin shafin
  • Yana kasancewa daya daga cikin dalilai dake kara karfin CEO.
  • Yana karawa appearance na nlogblog kyau, duk wanda ya ziyarci shafin zai so ya kara dawowa.
  • Shafukan blog kamar about, contact,  privacy policy da Terms and condition zasu kasance cikin tsari
  • Lebels,  tags da categories zasu kasance da kyau
  • Idan ka dora temple mai kyau a blog din ka, Archive na blog din zai tsaru yadda ya dace.

Illolin Rashin dora template mai kyau a blog

Template a blogger site yana da bukatan kyakkyawan template,  idan ya rasa shi ya zama rusashshe.
Daga cikin illolin rashin template mai kyau akwai wadannan;

  • Zai Gunduri maziyarta shafin; Idan template ya zama baida kyau ko a ka saka mishi wasu kaloli wadanda basu dace ba zai sa duk wanda ya ziyarci shafin ya kyamace shi kuma ba lallai bane ya iya sake dawowa.

  • Zai ragewa shafin trtraffic, Idan aka rasa masu ziyartan shafin, shafin zai rasa traffic, Traffic shine adadin ziyartan shafin.

Menene adsense?

Wannan shima darasi ne mai zaman kan shi domin yana da fadi sosai kuma akwai bukatan a haskawa mutane su fahimta sosai

Adsense hanya ce amintacciya wanda masu shafukan yanan gizo suke samun makodan kudade dashi, kamfanin google ne ya samar da wannan tsarin.

Akwai bayanai da dama akan wannan maudu'i zan yi cikakken bayani a kan shi a darasi na gaba.

Idan aka chanja template,  meye matsayain adsense dake site din❓


Read More: Ma'anar kalmar protocol a computer
Menene google analytics?
Yadda ake samun kudi ta internet ba tare da ka kir-kiri website ba
Yadda ake format din computer
Yadda za kasa password wa applications dake kan wayar ka
Sauke free Sora SEO template na Blogger
Amsar Wannan tambaya mai sauki ne kuma ga amsar kamar haka;
Chanja template kadai ba zai kawo matsala ba sai dai idan theme din yana kunshe da wasu abubuwa wadanda suka ci karo dokokin Google AdSense kafin zaka iya samun matsala.

Kafin ka chanja theme/template dole ne sai ka duba theme din da kyau domin ka tabbatar da cewa bai karya doka da ka'idoji na AdSense ba, bayan ka tabbatar da hakan sai ka Dora shi.

Chanja template a blogger site yana da wahala ne?

Chanja template a blogger baida wahala kowa zai iya chanjwa cikin sauki kuma a kankanin lokaci, ka daina tunanin wai baza ka iya ba.
Kasa a ranka cewa duk abunda wani yayi kai ma zaka iya.

Zan iya bawa wani ya dora min template a blogger site di na?

Eh idan baka iya ba zaka iya bawa wanda ka yadda dashi ya dora maka template.

Zaka iya tuntubar mu domin mu dora maka cikin farashi mai rahusa,  ka duba contact us akwai hanyar da zaka tuntube mu sai ka tura mana da sako ta wancan hanyar da muka bayar.

Ko kuma kayi comment da bukatar ka a kasan wannan post, zamu yi maka reply da zaran mun ga sakon.

Wannan shine karshen wannan darasin da fatan kun karu?
Ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi mai albarka don samun jin dadin ku.



Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK

Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP

Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER

Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM

Call & Message: +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post