Karanta wannan rubutu daga farko har zuwa karshe don warware wasu matsalolin dake iya faruwa game da tsarin dora talla na kamfanin google.
Kowa yasan cewa Google AdSense sune mafi inganci kuma masu biya ba tare da wata matsala ba ga bloggers, Mutane da dama suna irin Wannan tambayar Ta yaya zan samu approval na Google AdSense a blog site dina?
Karanta wannan: Abubuwa 3 da zakayi kafin kayi apply na google adsense
Samun Google AdSense a blogspot yana da matukar wahala don suna da tsauraran dokoki kuma daya daga cikin dokokin shine blog sai ya kai wata shida kafin su amince dashi har su sa masa talla a kai.
Ko da yake Wannan ba ko wane lokaci bane yake kasancewa haka, Idan ka kirkiri ingantaccen blog Zaka samu approved na AdSense cikin sauki.
saboda wasu dalilai Google AdSense basu fiye jin dadin blogspot bloggers ba Don wani da bazai iya cire kudi ya sayi domain ba sai yaje ya yita apply na Google AdSense, toh ya za a yi su dube ka Kai daka tsaya komai sai free?
Hosting free, domain ma haka bayan ga dubban mutane da suke sayan hosting da domain sai a baka a hana su? Idan kana bukatan approved ka sayi domain ta nan ne zaka fi samun karbuwa.
Sai dai kuma Akwai hanya mai sauki da zaka samu approved da domain na blogspot.
Karanta wannan: Kowa zai iya zama blogger?
Yadda zaka maida sunanka na facebook ya zama guda daya
How computer is working?
Koyi html, Css, Java script da programming cikin sauki a offline w3schools
Yadda waya take tura sakon kira zuwa wata wayar har ayi magana
Website guda 10 wadanda zaka iya yin karatunka na zamani a ciki
Idan ka tara post masu kyau daga 20 yayi sama Zaka iya samun approved. Amma idan ka sayi domain zaka fi samun karbuwa a gurin su.
Yanzu abun tambaya anan shine ta ya za a samu approved na AdSense a blogger:
Idan kana bukatan approve na google adsense cikin sauki ba tare da jan lokaci da yawa ba, ga abubuwan da za kayi;
- Ka sayi domain
- Ka kirkiri email address mai kyau
- Kayi pages kamar su about us, contact us, privacy policy da terms and conditions
- Ka tabbatar ka Dora template mai kyau
- Kayi post masu kyau da inganci kamar daga 10-15 sai dai daddaya ne suke samun approval a haka, mafi yawa sai post ya kai 30 zuwa sama suke samun adsense a shafukan su.
Sayan domain: Domain shine sunan shafin ka na yanan gizo, misali domain na BBC shine www.bbc.com, domain na Facebook shine www.Facebook.com, Nasan yanzu an fahimci ma'anar domain.
Bayan ka kirkiri shafin ka na yanan gizo wato blogger site yana zuwa ne da domain na kyauta, bayan sunan da ka zaba a lokacin da kake kirkiran blog din, a gaban za kaga .blogspot.com, misali idan 'asan' ka zaba toh zai kasance ne kamar haka www.asan.blogspot.com wannan shine domain din ka na kyauta.
Akwai wadanda suke neman google adsense da wannan domain na kyauta duk da ana iya samu amma sai an wahala sosai kafin a dace.
Abun da yafi shine ka sayi domain zaka fi samun approved, ai naka ma da sauki tunda domain ne kadai zaka saya, wadanda suke amfani da WordPress su sai sun sayi hosting da domain wanda kudi ne mai dan yawa.
Kai kuma da kake amfani da blogger ka samu saukin hosting don shi free ne a blogger domain ne kadai baza ka iya cire kudi ka saya ba?
Email address; Blogger kwata-kwata ma bazai kirkiru ba sai da email address haka adsense ma suna bukatan komai na site ya kasance cikin tsari, bayan ka sayi domain akwai yadda ake kirkiran email address wanda yake hade da sunan site din ka na blogger, misali info@sunandomain.com ko support@sunandomain.com
Kirkiran shafuka kamar su about, contact, privacy policy da terms and conditions; kirkiran wadannan shafuka (pages) yana da muhimmanci ba sai a wajen adsense kadai ba a'ah hatta masu ziyartan shafin ka zasu fi gamsuwa da kai kuma zasu yadda da kai.
Dalilin hakan kuwa shine su wadannan pages bayanai ne wanda suka kunshi mai blog ko website din, adireshin shi da kuma tsarin amfani da site din shi, idan babu wadannan shafukan adsense bazai kasance a wannan blog ba, mutane su ma ba lallai ne su gamsu da gaskiyar mai shafin ba.
Dora template mai tsari da kyau; Ka samu template wanda yake da zubi da tsari me kyau wanda duk wanda yazo shafin ka zai sake jin marmarin sake dawowa shafin.
Idan baka saka mai kyau ba maganar gaskiya itace baza rika samun maziyar ta ba kuma shafin da baya samun maziyarta masu yawa baya samun approve na adsense.
Karin bayani
Kar ka Dora hotunan da ba naka ba saboda basa bukatan hakan. Akwai website da yawa inda zaka samu hotuna na free ka Dora a blog din ka.
Nayi bayanin wasu website guda 11 wadanda zaka samu hotuna kyauta A nan.
Kayi design na site din ka da kyau, Kayi apply na AdSense ka more.
Zaka iya apply sau dayawa kafin su karbe ka, Duk lokacin da suka koro ka sai ka duba site din na ka kayi gyare-gyare ka kara post sai ka sake apply.
Ci gaba da kasancewa da wannan shafi don samun irin waddannan dama wasu rubutun.
Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK
Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP
Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER
Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM
Call & Message: +2349036117711
Tags:
ADSENSE
