Yadda zaka turawa abokin ka application ta watsapp cikin sauki












Wannan shafi mai albarka yau kuma yazo muku ne da cikakken bayanin yadda zaku tura ko wane irin application na waya da software na computer ta watsapp.


Karanta wannan: Yadda ake kasuwanci ta whatsapp

Ci gaba ya yawaita a wannan zamani don har koyarwa ake yi ta watsapp, idan za a yi amfani ne da wani application ko software ana iya tura shi ta watsapp din kuma ayi amfani dashi ba tare da samun tangarda ba.

Idan application ne na waya,  bayan an turo shi nan take ake installing ayi amfani dashi, idan kuma na computer ne kuma ya kasance wanda aka turawa da waya yake amfani nan ma ba matsala zai tura shi zuwa kan computer yaci gaba da amfani dashi.

Ya ake tura application ta watsapp❓

Wannan tambaya ce mai matukar muhimmanci domin akwai mutane da dama wadanda basu San yadda ake tura application ta watsapp ba, mutane sun kasu kashi biyu a Wannan bangare;

Kashi na farko sun San ana iya tura application wa wani ta watsapp sai dai basu San ta yadda ake turawa ba, kashi na biyu kuma kwata-kwata basu San ma za a iya tura application ta watsapp ba.

Ta yiwu akwai Wanda kake son turawa wani application kila babu shi a play store kuma ba kada link na Wannan application gashi Wanda kake bukatan turawa ba a kusa yake da kai ba kuma ka rasa hanyar da zaka bi ka tura mishi.

Toh Albishirin ka yau zan sanar da kai yadda zaka tura application ta watsapp ko a wane gari Wanda zaka turawa yake zai isa gare shi ya sauke kuma yayi installing yaci gaba da amfani dashi ba tangarda.


Karanta wannan: Yadda zaka kirkiri Gift android application da wayarka

Me ya kamata ka tanada kafin turawa abokin ka application ta watsapp?

Kamar yadda aka saba tura hotuna da video kai duk wani abunda ake turawa ma ta watsapp, kafin ka tura application ta watsapp sai ka mallaki wadannan;

  1. Mallakan Manhajar watsapp
  2. Data
  3. Application din da zaka tura
  • Manhajar watsapp; Manhajar watsapp shine application na watsapp, wanda kake amfani dashi don tura sakonni wa yan uwa da abokan arziki.
Bazai yiwu a iya tura ko ma wane irin sako ne ta watsapp ba tare da akwai application na watsapp a computer ko wayar mai yurawan ba, don more hira da tura manhajoji ta watsapp ga wanda baida shi, garzaya zuwa play store ka sauke shi ko kuma ka nemi wanda yake dashi ya tura maka.

Ba mai turawa bane kadai zai mallaki watsapp har wanda za a turawa, bazai yiwu ka turawa wanda baida watsapp application da ko wane irin sako ta watsapp ba.
  • Data;.Idan zaka tura sakon application, rubutu, hotuna da videos sai kana da data kafin sakon zai tafi gurin wanda ka turawa, idan baka da data bazai tafi ba, ko da akwai datan sai ka tura sako ba tare da ka kunna datan ba toh sakon bazai bar kan wayar ka ba har sai lokacin da ka kunna data.
Don haka kafin ka tura sako ta watsapp ka tabbatar akwai data, bayan akwai kuma ya kasance a kunne ta nan ne kadai sakon ka zai tafi.

Sai dai kuma duk da wadannan Idan babu network datar ma baza ta kunnu ba bare har ace sakon zai tafi, kafin sako ya tafi sai an kunna data kuma ya kasance da karfin network.

  • Application din da za a tura: bazai yiwu ka turawa wani abunda ba ka dashi ba, don haka kafin ka fara tunanin turawa dole ka mallake shi tuku.
Bayan ka mallake shi kuma kasan foldan da ka ajiye shi yanzu abunda ya rage kawai turawa ne, bayan network, da data.

Muhimmancin tura application/Sako ta watsapp

Tabbas tura application ko sako ta watsapp yana da matukar muhimmanci, kafin samun wannan ci gaba idan za a tura application ba a maganar watsapp sai an je kafa da kafa.

Saukin da aka samu a yanzu shine, ba sai an kashe kudin mota ko na mashin ba, babu batun neman kudin abinci ko gurin kwana, kana kwance a daki da wayar ka zaka tura sako komai nisan gurin.



Karanta wannan: Yadda zaka kirkiri android application na wall paper da wayar ka

Yadda zaka turawa abokin ka application ta watsapp

Idan zaka turawa wani application ta watsapp abu na farko da zaka fara yi shine ka shiga watsapp din ka Sai ka shiga gurin attach file wato gurin da nayi alaman kifiya a screen short dake kasa


Daga nan Zai kawo ka nan Sai ka shiga Document


Bayan ka shiga Document zai kai kai ka wani shafi sai ka shiga nan👇

Kana shiga zai nuna maka options Sai ka shiga storage Wanda ka ajiye wancan application ka taba kan shi sai ka zabi send nan take Zai tafi zuwa ga Wanda ka turawa.

Zaka iya kasancewa da wannan shafi don samun sauran rubutun mu dake tafe.




Facebook: YI LIKE A SHAFINMU NA FACEBOOK

Whatsapp: ZAKA IYA BIYOMU TA WHATSAPP

Twitter: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA TWITTER

Instagram: YI FOLLOWING DINMU A SHAFINMU NA INSTAGRAM

Call & Message: +2349036117711

Post a Comment

Previous Post Next Post